BADAKALAR WULAKANTA ALQUR’AN: Shawara Ga Wadanda Ake Zargi Da Mu kan Mu

Please follow and like us:

Zargin walakantarda Alqurani da akeyi ga wadannan jerin mutane: Hon. Ibrahim Tanko Chairman na Gusau, Hon. Mainasara Salisu Chairman Ward APC S/Gari Gusau da Hon. Ashiru Gusau Kansila S/Gari Ward. Wallahi ba karamin musifa bane, dole mu kare martabar Allah da maganar sa matukar muna son kawaunan mu da rahama. Innalilahi wainna ilaihi rajiun, lallai balai yakai bala’i mutum musulmi ya jefa qurani acikin Masai (toilet).

Tabbas Rayuwa tana cike da kalubale kala kala, daga cikin su akwai na alkahairi akwai kuma na Sharri. Rayuwar Dan Adam musulmi cike take da jarabawa kodai ya kasance jarabawa ta Alkhairi kota Sharri.

Yakamata da mu da wadanda ake Zargi mu sani, Komai soyayyar mu komi kiyayyar mu ga mutum musamman musulmi idan wata musiba ta afka masa zamu tashi taredashi mujajanta masa haka idan Alkhairi Ya same sa Zamu yi masa murna.

Duk soyayyar mu ga wadannan bayin Allah idan har muna son su da gaskiya tunda Zargi ya rigaya ya afka masu to ba za mu fa wanke su ba matukar ana tabbatar da wannan Zargi gare su za mu goyi bayan a hukunta su koda bamu so domin hukuncin shine ya dace kuma idan har an hukunta su suka yarda da hukuncin suka tuba Allah zai yafemasu.

Duk kuma yadda muke kiyayya da su kada mu rufe ido muna gurin wannan Zargi ya tabbata gare su matukar basu bane suka aikata mu roki Allah ya wanke su idan ba su bane domin kowanen mu na iya samun kan sa cikin kowane irin yanayi Allah ya sawaka.

Hanyar tuba ba zata taba rufewa mutum ba matukar bai mutuba komai girman laifi.

Shawara zuwa ga wadanda ake Zargi.

1. Ina ba wadannan bayin Allah shawara da su yi imani da Allah akan wannan abu daya afka ma su shine wajibi ne su yi imani da kaddara ta Alkhairi ko ta Sharri, koda su ne Su ka aikata koda kuwa ba su ne su ka aikata ba Matukar su na so su samu Sauki.

2. Kamar yadda Allah ya fada muna cewa aduk lokacin da dan Adam ya aikata wani aiki na Alkhairi daga Allah ne idan kuma mutum ya aikata wani aiki na Sharri to daga Mutum ne. Don haka idan Har su ne suka aikata wannan Abu to kada su dorawa kowa, su daura wa kan su su karbi hukunci su tuba gaskiyar tuba Allah Zai yafe masu. Idan kuma basu bane suka aikata to jarabawa ce su barma Allah kaffara ce a hakan Allah zai iya gafata masu.

3. Allah yana cewa “Aduk lokacin da ya jarabaci bawa da samun wata cuta to babu Wanda isa ya karkare masa wannan Cuta Sai Allah”. Haka kuma yazo muna a hadisi cewa “idan Duk duniya Zata Taru domin suyi nufin cuta ga bawa to babu abun da zai samu bawa sai abun da Allah ya rubuta gare shi”. Haka kuma akasin haka. Ya kamata da mu da su mu tuna wannan.

4. Ina ba wadannan bayin Allah Shawara kasancewar su Allah ya basu jagorancin Alummah ta bangare daban daban, kuma sai gashi wannan kaddara ta afka masu yana da kyau su dubi girman kujerun da suke rike dasu, su dubi girman Alummar da suke Shugabanta.

Kuma su dubi girman Zargin da ake yi masu, ina basu shawara duk yadda suke jin dadin wadannan kujeru dasu dangana su ajiye wadannan mukamai domin bada dama ga Sharia tayi aikin ta yanda ya kamata, domin kuma kare mutuncin Alummah da suke jagoranta.

Shawara ta zuwa ga mutane.

Ya kamata mutane mu sani idan ana Zargin mutum da aikata wani laifi matukar ba a gama wannan Shariar ba mu daina shiga gaban Shiria muna kokarin tabbatar da Zargi ko kore zargi ga wadanda ake tuhuma.

Ya faru alokacin Manzon Allah (S.A.W) da aka yiwa Aisha (R.A) Matar Annabi S.A.W Zargin da kazafin Zina duk soyayyar ta ga Mijin ta da uwanyen ta basu wanketa ba, haka basu tabbatar da Zargin ba Har Saida Allah ya wanke ta kuma komai ya wuce wadanda suka Zarge ta suka ji kunya wasu suka tuba.

To idan har Za’a Zargi Matar Manzon mu (s.a.w) wanene zai kauce wa Zargi?

Mu daina yada kalaman batanci ga junan mu, mu rika gurin alkahairi ga junan mu, mu kiyaye iyakokin Allah.

Ya zama wajibi gare mu mu kare martabar Alqurani koda Zargi ya fada ga kawunan mu, iyayen mu, yan uwan mu, masoyan mu, koma makiyan mu.

Idan har abun da ake Zargin su Sun aikata duk yanda muke son su yanke masu hukunci ya zama wajibi.

Idan kuma basu aikta ba duk yadda bamu son su ya zama wajibi mugoyi bayan wanke su.

Allah ya kare mu daga miyagun kaddarori.

Daga Ubaidullah Yahya kaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *